Labarin kwallon kafa: Crystal palace ta kori kocin ta

Crystal Palace ta kori kocin ta (PA)

Palace ta kori De boer bayan wasan da ta buga ranar lahadi da Burnley wanda Burnley taci nasara

Crystal palace ta kori kocin ta Frank De Boer bayan kwana 77 da nada shi a matsayin mai horaswa.

A karkashin jagorancin dan kasar Holland ƙungiyar Crystal Palace bata samu maki daya kuma bata sa ƙwallo ko daya a raga cikin wassanin huɗu da ta buga na Firimiya.

 

Bayan wasan da ta buga ranar lahadi ne Palace ta yanke shawarar koran shi kuma tana shirin daukan tsohon kocin tawagar ƙasar Ingila Roy Hodgson ya maye gurbin De Boer.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

from LexxyTech Corporation http://ift.tt/2eQpPAw

Post a Comment

0 Comments