Tambuwal da Yari: Gwamnatin jihar Sokoto da Zamfara sun hada gwiwa wajen gyaran titin sokoto zuwa Gusau

gwamna Aminu Tambuwal

Titin wanda ya hada da Sokoto, kebbi, Zamfara da Katsina a kan kudi naira miliyan 100

Gwamnatin jihar Sokoto da Zamfara sun kammala gyaran babban titin da ya hada jihohi don magance matsololi da ake fuskanta a hanyar

Kakakin gwamnan jihar Sokoto Mallam Imam Imam ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ma manema labarai ranar litinin 11 ga watan Satumba a Sokoto.

Titin wanda ya hada da Sokoto, kebbi, Zamfara da Katsina a kan kudi naira miliyan 100.

“Jihohi sun hada gwiwa wajen gyaran wannan titin wanda hada babban birenen jihohin harda wasu jihohi. Wannan titin yana cikin muhimmiyar tituna dake yankin arewa maso yamma don ya dangana da jamhoriyar Nijar” inji kakakin.

Gwamna Abdulazeez Yari na Zamfara ya dauki nauyin gyaran sashen Gusau zuwa Tureta na titin shi kuma gwamnatin Aminu Tambuwal ta kammala sashen Tureta zuwa garin Sokoto.

 

A cikin bayanin da aka fitar jihohin zasu bukaci gwamnatin tarayya da ta mayar masu da kudin gyaran da suka yi kasancewa titin na gwamnatin tarayya ne.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

from LexxyTech Corporation http://ift.tt/2wU4ukg

Post a Comment

0 Comments