Muhammadu Buhari: Dole ne mu mayar da martaban kasa a fannin safarar kayan abinci kasashen waje

President says Nigeria must regain its pride in food exportation

Shugaban ya sanar da haka yayin da ya karbi bakonci wasu yan jam'iyar APC na jihar Kebbi a fadar sa na Villa

A ranar juma'a 29 ga wata shugaban kasa Muhammadu BUhari ya sanar cewa gwamnatin tarayya zata iya bakin kokarin ta wajen bunkasa fanin noma a kasar domin mayar da martaban ta a bangaren safarar kayan abinci kasashen waje.

Shugaban ya sanar da haka yayin da ya amshi bakoncin tawagar yan jam'iyar APC reshin jihar Kebbi wanda gwamnan jihar Alhaji Atiku Bagudu ya jagoranta.

A jawabin sa, shugaban ya sanar cewa dokar hana shigowa da shinkafa ya taimaka wajen rage sufurin da ake yi na abincin.

Shugaba Buhari yace harkar noma yana cigaba da bunkasawa a yankunan jihar Kano da Kaduna da katsina da Sokoto kana abun farin ciki ne ganin matasa ke kan gaba a sana'ar.

Shugaban ya sanar cewa gwamnatin sa zata cigaba da kokari wajen bunkasa bangaren ilimi da kiwon lafiya domin kasar ta kasance mai takama da sauran kasashn duniya.

Karanta>> Jiga-jigan yan siyasa sun tura ma iyalin shugaban kasa Sakonnin jaje

Yayin da yake gabatar da bakin da suka ziyarci shugaban babban ministan shari'a Abubakar Malami ya jinjina wa shugaban bisa ga yunkurin da yake wajen bunkasa harkar noma a kasar.

Gwamna Bagudu tare da mukaerabben shi ciki harda tsohon gwamnan jihar Kebbi Usman Dakingari da yan goyon bayan wadanda suka sauya sheka daga jam'iyar PDP zuewa APC sun jajenta wa shugaban bisa ga hatsarin da dan shi Yusuf Buhari ya samu.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

from LexxyTech Corporation http://ift.tt/2Ccm9Hr

Post a Comment

0 Comments