Muhammadu Buhari: Shugaban ya nada matattu cikin sabon nade-nade da yayi

President says Nigeria must regain its pride in food exportation

Wannan labarin ya janyo tsegumi ga yan kasa inda yan nijeriya ke ta kokawa a kafafen sada zumunta.

A cikin jerin nadin mukami da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ranar juma'a na masu ruwa da tsaki 209 da membobi 1258 ciki akwai wasu matattu.

Wannan labarin ya janyo tsegumi ga yan kasa inda yan nijeriya ke ta kokawa a kafafen sada zumunta.

Cikin matattun akwai Cif Donald Ugbaja wanda aka nada a matsayin memba na Consumer Protection Council, alhali ya rasu tun ranar 29 na watan Nuwamba 2017.

Hakazalika an nada Revarend Christopher Utov wanda aka nada shi a matsayin memba na cibiyar bincike kan walwala da kasuwanci na kasa, bayan shima ya rasu ne cikin watan maris na 2017.

Shima dai Francis Okpozo wanda tsohon dan majalisa ne a jumhoriya ta biyu kuma tsohon jigo na jam'iyar APC, ya samu matsayin shugaban Nigerian Press Council.

Shi dai Okpozo ya rasu ne a garin Benin city washe garin bayan ranar kirismeti na 2016 wanda har shi shugaban kasa ya tura ma iyalen sa sakon ta'aziya.

Wannan sabon lamarin wanda mawuyaci ne a same shi a tarihin shugabancin kasar ya sa yan Nijeriya mamaki tare da jawo tsegumi kan mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

A kafar sadarwa ta Twitter wasu yan kasar sun tofa albarkacin bakin su game da nadin mukami ga mattatu da shugaban yayi inda akasari suna ta kushe gwamnatin shi.

Mafi yawanci suna ganin cewa gwamnati wanda take yunkurin wanzar da cin hanci da rashawa ta gaza aiwatar da yunkurin ta.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

from LexxyTech Corporation http://ift.tt/2Cqe7K5

Post a Comment

0 Comments