An garzaya da dan majalisar wata asibitin kudi dake nan Abuja domin samun kulawar raunin da ya samu yayin da yan sanda ke shirin tafiya dashi jihar Kogi
Dan majalisar dattawa Dino Melaye wanda ke fuskantar tarzoma daga jami'an tsaro yayi wani abun ban mamaki yayin da ya dira daga mota mai tafiya kuma ya tsare cikin daji domin tsare daga hannun jami'an tsaro dake jigilar shi.
A safiyar ranar talata rundunar SARS suka cafke dan majalisar a nan gidan shi dake Abuja bisa zargin da ake masa kan wasu laifufuka da ya danganci daukar nauyin wasu yan tawaye.
Kamar yadda labarai suka bayana, dan majalisar yayi hayaniya da jami'an tsaro kafin ya kufce daga hannun su a hanyar su na wucewa dashi jihar Kogi.
Jami'an sun sanar cewa zasu tafi dashi wata kotu dake nan Abuja sai dai daga baya suka canza alkiblar tafiyar inda suka nufa hanyar jihar Kogi wanda bisa wannan dalilin sanatan ya dira daga mota har ya nufi daji.
Zuwan shi asibiti
Jim kadan bayan abun da ya faru da sanatan anyi gaggawa dashi asibiti domin samun kulawa kan raunin da yaji yayin da ya dira daga motar yan sanda.
A daidai misalin karfe 4:25 na rana aka garzaya dashi cikin makara zuwa asibitin Zankli medical Center dake nan Mabushi na garin Abuja
from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online
from LexxyTech Corporation https://ift.tt/2HYl0D3

1 Comments
razer surround pro
ReplyDelete